A jiya Jumma'a 7 ga wata da dare, agogon kasar Rasha ne aka bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu karo na 22 a birnin Sochi, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halartar bisa goron gayyatar takwaransa na kasar ta Rasha Vladimir Putin.
Wannan ita ce ziyarar shugaba Xi Jinping ta farko zuwa kasashen waje, a wannan shekara, ko da ya ke a watan Maris na shekarar 2013, ya ziyarci kasar ta Rasha kwanaki kadan bayan ya zama shugaban kasar ta Sin.
Bugu da kari, wannan shi ne karon farko da wani shugaban kasar Sin ya halarci bikin bude manyan wasanni a kasashen waje
Shugaba Xi ya jinjinawa tawagar kasar Sin da Tong Jian ya jagoranta yayin da suka shigo filin wasan. Kasar ta Sin dai ta tura tawaga mai kunshe da mutane 138, ciki har da 'yan wasa 65, inda za su fafata a wasanni daban-daban. Tun da farko sai da shugaba Xi ya gana da 'yan wasa da masu horas da su, inda ya karfafa musu gwiwar cewar, Sinawa na mayar da hankali sosai a kansu, ganin cewa sun yi tattaki har zuwa Rasha don halartar wannan gasa a lokacin bikin bazara.
Shugaba Putin na Rasha ne ya bude gasar a filin wasa na Fisht da ke garin na Sochi, bayan jawabin shugaban hukumar shirya gasar wasannin Olmpics ta duniya Thomas Bach, wanda ya jaddada manufar gasar a matsayin wata gada da ke hallara jama'a waje guda. (Ibrahim)