in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai kai ziyarar aiki a kasar Pakistan
2015-04-17 09:15:15 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Pakistan daga ranar litinin 20 zuwa ranar tarlata 21 mako mai zuwa, kamar yadda Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Lu Kang ya sanar a safiyar Jumma'a.

Lu Kang ya ce wannan ziyara ta biyo bayan gayyatar da shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain da kuma firaministan kasar Mian Muhammad Nawaz Sharif suka yi ma Shugaba Xi ne.

Haka kuma, a ranar Talatan 21 ga wata Shugaba Xi daga Pakistan zai wuce kasar Indonesia bisa gayyatar Shugaba Joko Widodo na kasar domin halartar taron shugabannin Asiya da Afrika da kuma bikin tunawa da ranar cika shekaru 60 da bude taron Bandung daga ranar 21 zuwa ranar 24 ga wata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China