in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun jajantawa takwarorinsu na kasashenJamus da Spaniya
2015-03-26 11:11:23 cri
A jiya Laraba 25 ga watan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping,ya bayyana sakon jajensa ga takwaransa na kasar Jamus Joachim Gauck, da na kasar Spaniya Felipe VI, game da hadarin jirgin saman kamfanin Germanwings.

A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'ata da shikansa, Shugaban Xi ya gabatar da ta'aziyyar mutanen da suka riga mu gidan gaskiya, tare da janjantawa iyalai da danginsu.

Haka kuma,a wannan rana, firaministan Sin Li Keqiangshi ma, ya bayyana jaje ga takwararsa ta Jamus Angela Merkel, da na kasar Spaniya Mariano Rajoy, game da hasarar rayukan da aka samu a hadarin jirgin sama na Germanwings.A madadin gwamnatin Sin da jama'arta, y a bayyana matukar juyayi ga rasuwar mutanen, tare da janjanta wa danginsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China