A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Yarima William wato Duke of Cambridge na kasar Ingila a babban dakin taron jama'ar kasar Sin.
A bokacin ganawarsu, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasashen Sin da Ingila su manyan kasashen duniya ne, da suke da moriya bai daya a fannoni da dama, kuma suna daukar nauyin kiyaye zaman lafiya da neman samun bunkasuwar duniya. Xi ya kara da cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na gudana yadda ya kamata, dangantakarsu ta abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tana samun saurin bunkasuwa.
A nasa bangaren, Yarima William ya mika wa shugaba Xi Jinping wasikar gayyata da sarauniyar Ingila Elizabeth II ta aiko, inda sarauniya ta ce, tana sa ran shugaba Xi zai kai ziyara a kasar Ingila. Ban da haka kuma, yarima William ya bayyana cewa, a shekarun baya, kasashen biyu sun raya huldar ciniki sosai a tsakaninsu, kuma sun yi cudanya sosai a fannin al'adu.(Lami)