in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun mai da hankali kan samun bunkasuwa tare, a yayin taron dandalin tattaunawa na Boao a shekarar 2013
2013-04-07 20:44:21 cri

Ranar Asabar 7 ga wata, a garin Boao na lardin Hainan na kasar Sin, an bude taron dandalin tattaunawa na nahiyar Asiya na shekarar 2013, wanda a kan shirya a ko wace shekara, inda kuma jami'an gwamnatoci da wakilan rukunonin masana'antu, kasuwanci da ilmi daga kasashe da yankuna 43 na duniya, suke tattaunawa tare, bisa babban jigon "neman samun bunkasuwar nahiyar Asiya baki daya, ta hanyoyin yin kirkire-kirkire, da sauke nauyi da kuma yin hadin gwiwa".

A cikin jawabinsa a yayin bikin bude taron, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi fatan cewa, kasashen duniya za su tsaya kan yin kokarin tare a halin yanzu, a yunkurin daga nahiyar Asiya, da ma duk duniya zuwa sabon mataki.

A cikin jawabinsa mai lakabin "yin kokarin samar da kyakkyawar makoma a Asiya da ma duniya baki daya", shugaba Xi Jinping ya ce, yanzu an shiga sabon mataki na kyautata tattalin arzikin duniya. Nahiyar Asiya da sassa daban daban na duniya, suna hada kai sosai wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya, matakin da ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado, da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya. Sa'an nan kuma, kamar yadda ake yi a sassa daban daban na duniya, ya zuwa yanzu nahiyar Asiya ita ma tana fuskantar kalubaloli daban daban, ta fuskar samun bunkasuwa.

shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda hudu a cikin jawabinsa, wato kamata ya yi bangarori daban daban su yi kokarin yin kirkire-kirkire, don sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da yin hadin gwiwa wajen kiyaye zaman lafiya, don tabbatar da tsaro yayin da ake kokarin samun ci gaba, da kara hadin gwiwa don samar da hanyoyi wajen sa kaimi ga samun ci gaba, da kuma ci gaba da bude kofa, da amincewa da bambancin juna don samar da sharadi wajen samun bunkasuwa tare. (Tasallah&Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China