Ranar 27ga wata, a nan Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi shawarwari da takwararsa Madam Park Geun-hye ta kasar Korea ta Kudu.
A yayin shawarwarin, mista Xi ya ce, kasar Sin na sa muhimmanci sosai kan huldar da ke tsakaninta da Korea ta Kudu, ta kuma mayar da ita a wani muhimmin matsayi a yayin da take kula da huldar da ke tsakaninta da kasashen duniya. Shugaban ya kara da cewa, yana son yin kokari tare da madam Park Geun-hye wajen kara raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare yadda ya kamata, a kokarin kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri.
A nata bangaren, madam Park Geun-hye ta ce, kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da tsaro da manyan tsare-tsare na da muhimmanci sosai, haka kuma, inganta mu'amalar al'adu a tsakanin jama'ar kasashen 2 shi ma haka, saboda yin mu'amala a tsakanin mutane kan kyautata dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen 2. Ta haka ta ba da shawarar kafa kwamitin hadin gwiwar kasashen 2 mai kula da yin mu'amalar al'adu, wanda zai sa kaimi kan yin mu'amala a tsakanin matasa da kananan hukumomi da kuma masu ilmi.(Tasallah)