in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hirar da shugaban Sin ya yi da manema labarai a Sochi ta samu tsokaci da dama
2014-02-10 11:14:32 cri

Rahotanni na nuna cewa, hirar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ta baya bayan nan da kafar talabijin na Rossiya lokacin da ya halarci bikin bude wasannin Olympics na lokacin sanyi a Sochi na kasar Rasha ya jawo tsokaci daga jama'a da dama na kasashen duniya.

Shugaba Xi ya yi hira ta musamman da talabijin na Rossiya dake Sochi a kudancin Rasha a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce, ya gamsu kwarai da huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan hirar ta shugaba Xi ta nuna aniyar cigaba da abota da hadin gwiwwa da kasar Rasha, abin da ya tabbatar da kokarin kasar Sin na ganin ta kara zurfafa kwaskwarimarta, in ji wasu malaman kasashen waje da Xinhua ta zanta da su game da ra'ayinsu a kan hirar shigaba Xi.

Yakov Berger, wani babban masani a fannin nazari mai zurfi kan huldar kasa da kasa na kasar Rashan, ya ce, shugaba Xi ya yi bayani a kan kokarin kasar wajen zurfafa kwaskwarima.

A cewar shi, a takaice dai, cikin hirar da aka yi da shugaban na kasar Sin, ya mai da hankali ne a kan muhimmancin kasuwa a cikin tattalin arzikin Sin. Kuma an kafa hukumar da za ta kula da hakan karkashin jagorancin shugaban kasar.

Ya yi bayanin cewa, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta na shawo kan wahalhalun da take fuskanta, sannan ta ingiza yin kwaskwarima domin ganin cimma mafarkin jama'ar kasar Sin tare da tabbatar da farfadowar kasar yadda ya kamata. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China