Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya shaidawa ministoci da gwamnonin lardunan kasar, da su yi amfani da kwarewarsu wajen zamanantar da ayyukan gwamnatin kasar.
Xi ya yi wannan kira ne ranar Litinin 17 ga wata, yayin da yake jawabi a taron karawa juna sani da makarantar nazarin zurfafa ayyukan gyare-gyare na kwamitin tsakiya ta JKS ta shirya, kamar yadda cikakken zama na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 ya bukata.
Shugaba Xi ya shaidawa mahalarta taron cewa, manufar JKS ita ce, lalubo managarciyar hanyar ci gaba, inganta rayuwar jama'a da samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin al'umma.
Ya ce, za a cimma dukkan wadannan ne, idan har jam'iyya da jami'ai suka kasance masu kima da kwarewa, ta yadda za a daga daraja da karfin ayyukan jam'iyya, sassa da hukumomin gwamnati, masana'antu da kuma kungiyoyin fararen hula. (Ibrahim)