Xi Jinping ya halarci bikin rufe taron shugabannnin masana'antu da kasuwanci na kungiyar APEC
A ran 7 ga wata a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci bikin rufe taron shugabannnin masana'antu da kasuwanci na kungiyar APEC, a cikin jawabin da ya gabatar mai taken 'kasar Sin za ta kara zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga duniya, domin wadatar da nahiyar Asiya da tekun Pacific', ya jaddada cewa, kasar Sin tana samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, ta yadda za ta kara samar da kyakkyawar dama ga nahiyar Asiya da tekun Pacific suma su samu bunkasuwa.
Shugaba Xi wanda ya nuna imani ga kyakkyawar makomar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin,ya ce, kasar tana tsara babban shiri domin zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga duniya,
Haka kuma inji shi kasar Sin tana fatan hadin gwiwa tare da abokai da ke nahiyar Asiya da tekun Pacific, domin wadatar da wannan nahiyar.(Danladi)