in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya isa kasar Costa Rica
2013-06-03 14:30:54 cri

A ranar 2 ga wata agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa San Jose babban birnin kasar Costa Rica domin ziyarar aiki.

Mr Xi bayan saukar sa, ya nuna cewa, Costa Rica muhimmiyar kasa ce a tsakiyar nahiyar Amurka, don haka yana fatan yin musayar ra'ayi da shugaba Laura Chinchilla Miranda da sauran kusoshin kasar kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da wasu manyan batutuwa dake jawo hankalinsu.

Haka kuma Mr Xi ya yi imani da cewa, kasashen biyu za su amince da juna a fannin siyasa, habaka hadin gwiwa, zurfafa zumunci da kawo moriyar juna sakamakon wannan ziyara. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China