An kafa yankunan ciniki cikin 'yanci a lardunan Guangdong, Jujian da birnin Tianjin a safiyar Yau Talata 21 ga wata, abin da ya alamanta cewa, an kara yawan irin yankuna ban da wanda aka kafa a birnin Shanghai a da. Bisa tsarin da aka gabatar a kwanan baya kan wadannan yankuna, za a bunkasa wadannan yankuna gaba daya don kara karfin bude kofa ga kasashen waje. Habakar yankunan ciniki cikin 'yanci a wannan karo ya bayyana niyyar da Sin ke dauka wajen zurfafa yin kwaskwarima a karin wasu wurare da daukaka manufarta ta bude kofa ga kasashen waje. (Amina)