A gun taron manema labaru na majalisar gudanarwa da aka yi a wannan rana, kakakin hukumar kwastam ta Sin Huang Songping ya yi nazari, inda ya bayyana cewa, har yanzu, ana kokarin daidaita tattalin arzikin duniya bayan da aka samu rikicin kudi, wanda ya sa ba a farfado da tattalin arziki sosai ba, kuma da kyar za'a iya warware wannan batu gaba daya. A sa'i daya kuma, akwai yiwuwar koma bayan tattalin arzikin kasar Sin, yawan kudin da Sin ta samu wajen shige da ficen kayayyaki ya ragu, amma ingancin cinikin da Sin ta yi da kasashen waje ya samu kyautatuwa.
Mr. Huang ya yi nuni da cewa, duk da cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen kyautata ingancin cinikin da ta yi da kasashen waje, tare da kyautata tsarin yin ciniki, sai dai har yanzu Sin na fuskantar matsaloli da dama wajen raya sha'anin cinikayya da kasashen waje.(Bako)