An kafa yankin gwajin ciniki cikin 'yanci na Tianjin na kasar Sin a Talatar nan a unguwar Dongjiang ta birnin Tianjin. A matsayin yankin gudanar da ciniki cikin 'yanci na farko a arewacin kasar Sin, yankin na da nauyin ingiza bunkasuwar biranen Beijing, da Tianjin, da kuma lardin Hebei gaba daya domin kara karfinsu a fannin ciniki a duniya.
Magajin garin Tianjin Huang Xingguo ya ce, a halin yanzu, an sake yin kwaskwarima ga tsarin cinikayya na duniya, don haka ake kara bukatar bude kofa ga kasashen waje. Yankin gwajin ciniki cikin 'yanci na da muhimmiyar ma'ana a fannin bude kofa ga kasashen waje, domin samun zarafi mai kyau na raya tattalin arziki.(Lami)