Kawo yanzu dai, aikin fitar da na'urorin layin dogo zuwa ketare daga kasar Sin, ya riga ya zama wani sabon aikin dake sa kaimi ga karuwar cinikayyar ketare.
Tun lokacin da kasar Sin ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya WTO a shekara ta 2011, aikin fitar da na'urorin layin dogo daga kasar ya yi saurin karuwa, kana yawan kudin cinikayya ta hanyar fitar da jiragen kasa zuwa ketare, ya karu daga dala miliyan 80 a shekarar 2001, zuwa dala biliyan 3.74 a shekarar 2014.
Haka zakila, bisa kididdigar da aka fitar, kasar Sin ta fitar da na'urorin layin dogo zuwa kasashe, da yankuna fiye da 80 da ke nahiyoyi shida. Wadanda suka hada da wasu kasashen nahiyar Asiya, da Argentina, da Australia, da Amurka wadanda ke cikin muhimman kasuwanni a wannan fanni. Kana jimillar kudaden da aka samu daga wannan hada-hada, sun zarce kashi 50 cikin dari bisa na dukkan jimillar kudaden da Sin ta samu, karkashin cinikayyar fitar da na'urorin layin dogo zuwa ketare.(Kande Gao)