Bisa kididdigar, tun daga watan Yulin shekarar 2013, zuwa karshen watan Disambar bara, an gudanar da cinikin fitar da kayayyakin Sin zuwa kasashen waje ta hanyar amfani da internet a birane 16, kamar Shanghai, da Chongqing, da Hangzhou, da Ningbo da sauransu. Inda yawan kudin da aka samu daga wannan hada-hada ya kai sama da Yuan biliyan 2, kana yawan kasashe da yankunan da suke yin ciniki ya kai 181.
Haka zalika kuma, an fara gudanar da cinikin shigar da kayayyaki daga kasashen waje, zuwa kasar Sin ta hanyar internet a biranen Shanghai, da Chongqing, da Hangzhou, da Ningbo, da Zhengzhou, da Guangzhou da kuma Shenzhen. (Zainab)