An kaddamar da yankin gwaji na gudanar da ciniki cikin 'yanci na lardin Guangdong dake nan kasar Sin a unguwar Nansha ta birnin Guangzhou. Sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin a lardin na Guangdong Hu Chunhua, shi ne ya sanar da kaddamar da yankin a hukunce.
Shugaban lardin Guangdong Zhu Xiaodan ya bayyana cewa, lardin Guangdong dai na kan gaba a fannin gudanar da manufar gyare-gyare, da bude kofa ta kasar Sin.
Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da kudurin kafa yankin ciniki cikin 'yanci a lardin, domin zurfafa hadin gwiwa a tsakanin lardin Guangdong da yankunan Hongkong da Macao. Yankin gwaji na gudanar da ciniki cikin 'yanci na lardin Guangdong, ya kunshi unguwoyin Nansha da Shekou, da kuma Hengqin.
Bisa shirin da aka yi, unguwar Nansha za ta dukufa a fannin cinikin kasashe masu wadata, kuma za ta mai da hankali kan aikin ba da hidima ga masana'antu irin na zamani. Kana unguwar Shekou za ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin lardin Guangdong, da yankunan Hongkong da Macao, da kafa tashar kasa da kasa ta bude kofa ga kasashen waje. Haka zalika, unguwar Hengqin za ta dukufa kan hadin gwiwa tsakanin lardin Guangdong da yankin Macao da aikin ba da ilmi, da raya al'adu, da ba da kyakkyawar hidima ga aikin kasuwanci da yawon shakatawa, tare da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Macao. (Lami).