Wasu tagwayen bama-bamai da suka tarwatse cikin wata mota a birnin Mogadishun kasar Somaliya, sun hallaka sama da mutane 20, ciki hadda 'yan majalissar dokokin kasar 2, tare da raunata mutane da dama.
Mahukuntan kasar sun ce cikin wadanda suka jikkata yayin harin na ranar Juma'a hadda mataimakin firaministan kasar.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan kasar Qasim Ahmed ya ce harin ya ritsa da wani jigo a gwamnatin yankin Banaadir, an kuma garzaya da mutane da dama zuwa asibiti sakamakon raunukan da suka samu.
A wani ci gaban kuma ministan watsa labarun kasar Mohamed Abdi Hayir Mareye, ya yi Allah wadai da tashin bama-baman, ya na mai cewa gwamnatin kasar za a gudanar da bincike.
Tuni dai kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamar da harin.
Harin na wannan karo dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaurara matakan tsaro, gabanin ziyarar da shugaban kasar Djibouti zai gudanar a kasar.
A baya bayan nan dai 'yan sandan Somaliyan na fadada ayyukan su na yaki da masu tada kayar baya. Inda rahotanni ke cewa 'yan sandan sun hallaka wani magoyi bayan kungiyar, tare da kame wasu da dama.