Sharmarke ya ce gwamnatinsa za ta aiwatar da manufofi, da za su taimakawa gudanar ayyukan hukuma bisa gaskiya da amana. Kaza lika firaministan na Somaliya ya alkawarta kafa gwamnati mai kunshe da mambobi 25, wadda zata share fagen gudanar tsaftataccen zabe a kasar.
Ya ce sabuwar gwamnatin za ta maida hankali ga wanzuwar zaman lafiya da lumana, tare da kwato sauran yankunan kasar da kungiyar Al-shabaab ke iko da su. Baya ga batun tabbatar da managarcin tsarin siyasa, da inganta tsarin gwamnatin tarayya, tare da dinke barakar dake tsakanin sassan kasar.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Alhamis din da ta gabata ne aka gudanar da bikin mika takardun aiki ga Sharmarke, wanda ya maye gurbin tsohon firaministan kasar Abdiweli Sheikh Ahmed.