in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi allawadai da harin da aka kai a wani ginin otel da ke birnin Mogadiscio
2015-02-21 16:56:16 cri
Da babbar murya ce, MDD ta yi allawadai a ranar Jumma'a da wani harin ta'addancin da aka kai a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somaliya, harin da kungiyar Al-Shabab da ke mubaya ga kungiyar Al-Qaida ta dauki alhakin kai wa.

A cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa, sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi tir da allawadai da harin da aka kai a Central Hotel, otel din da ke unguwar Hamar Weyne da yawancin manyan jami'an gwamnati da 'yan kasashen waje ke yawan shiga. Harin ya halaka mutane akalla 20 tare da jikkata wasu da dama, kuma ya faru ne a yayin da mambobin gwamnatin kasar Somaliya, daga cikinsu mataimakin faraminista, da wasu 'yan majalisa suke gudanar da wani taro a otel din.

A cikin wata hira ta wayar tarho bayan abkuwar lamarin tare da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud, mista Ban Ki-moon ya bayyana juyayinsa da ta'aziya ga gwamnati da iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Haka kuma, sakatare janar na MDD ya jinjinawa jami'an tsaron kasar Somliya, da ke samun nasara kan wannan matsala, tare da jaddada goyon bayan MDD wajen ci gaba da tallafawa al'umma da gwamnatin Somaliya, da ke aiki tukuru wajen gina zaman lafiya da samun ci gaban kasarsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China