Wata sanarwa da ta fito daga ofishin UNICEF dake Nairobi ta kasar Kenya ya ce za'a kammala yarjejeniyar da zaran gwamnatin ta Somaliya ta gabatarwa MDD alkaluman da ake bukata na amincewa da yarjejeniyar.
Sanarwar ta ce sanya hannu da Somalia ta yi a kan dokar 'yancin yara tamkar saka jari ne ga makomar yaran kasar ta Somaliya kuma hakan yana nufin yaran kasar ta Somalia a yanzu sun samu 'yanci a karkashin doka wacce gwamnatin kasar zata yi amfani da ita wajen samar da ci gaba da kariya ga yaran kasar.
Sanarwar ta kara bayyana cewar a yanzu ya zama dole dokokin kasar su zamanto suna bin tsarin dokar 'yancin yara na duniya kuma kasar ta zamanto kasa ta 194 daga jerin kasashe na duniya da suka rattaba hannu akan dokoki na 'yancin yara.
A halin da ake ciki dai yaran kasar ta Somaliya na ci gaba da fuskantar kalubale musamman saboda rikice-rikice da ya addabi kasar da kuma matsaloli na cututtuka da karancin abinci masu gina jiki.
A shekarar 1989 ne babban taron MDD ya amincer da dokokin 'yancin yara na MDD.(Suwaiba)