in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Somaliya ta amince da sabuwar majalisar zartaswar kasar
2015-02-10 14:19:34 cri
A jiya Litinin ne majalisar dokokin kasar Somaliya, ta amince da jerin sunayen 'yan majalisar zartaswar kasar, wadanda sabon firaministan kasar omar Abdirashid Ali Sharmarke ya gabatar mata. Majalissar ministocin dai na kunshe ne da mutane 66, da suka hada da ministoci 26.

Shugaban majalisar dokokin kasar Farfesa Mohamed Osman Jawari, ya ce cikin 'yan majalisar su 220 da suka kada kuri'u game da kudurin, 191 sun amince da hakan, lamarin da ya nuna imanin da majalisar dokokin ke da shi ga sabuwar majalisar ministocin.

Tuni dai aka rantsar da sabbin 'yan majalissar zartaswar kasar, wadanda za su jagoranci hukumomin gwamnati wajen tabbatar da burin bunkasuwa na shekarar 2016, ciki hadda aikin tabbatar da nasarar kafa hukumar zaben kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China