Hukumar leken asiri da tsaron kasar Somaliya ta bayar da sanarwa a wannan rana, inda ta bayyana cewa, sojojin kasar Amurka sun kai hari ta sama kan sansanin mayakan kungiyar Al Shabaab dake kudancin kasar Somaliya a ranar 31 ga watan Janairu, kuma shugaban kungiyar dake kula da harkokin gudanar da ayyuka da leken asiri Yusuf Dheeq da wasu manyan jami'an kungiyar sun mutu a sakamakon harin.
Sanarwar ta kara da cewa, Yusuf Dheeq yana da hannu a hare-hare da dama da aka kai a kasar ta Somaliya.
Har zuwa yanzu dai, kungiyar Al Shabaab ba ta bayar da wata sanarwa game da hari ta sama da sojojin Amurka suka kai ba. (Zainab)