in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 6 sun rasu sanadiyyar fashewar boma-bomai a Somaliya
2015-01-05 14:07:42 cri
Hukumar tsaron kasa ta Somaliya ta gaskata a ran 4 ga wata cewa, a wannan rana, wasu boma-boman da aka dana cikin mota sun fashe a wani wurin dake kusa da wani sansanin sojan dake Mogadisho, babban birnin kasar, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda shida, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kakakin hukumar tsaron kasa ta Somaliya Mohammed Yusuf ya bayyana cewa, lamarin fashewar boma-boman da maharan suka aikata a sansanin rundunar sojan din ya tashi hankulan mazauna wurin sosai.

Wasu da lamarin ya faru gaban idanunsu sun bayyana cewa, fashewar boma-bomai ta lalata motoci guda hudu, da dukiyoyin jama'a.

Kungiyar tsattsauran ra'ayi ta "Somali Youth Party" ta sanar da daukar alhakin lamarin, domin mai da martani ga gwamnatin kasar da sojojin kasar Amurka, wadanda suka kai musu hari ta sama a kwanan baya, inda suka halaka shugaban kungiyar Ahmed Abdi Godane da kuma shugaban sashen leken asiri na kungiyar Abdi Shakour. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China