Mr. Ban wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da sabon firaministan ta wayar tarho, ya kuma ja hankalinsa game da bukatar da ake da ita, ta gaggauta kafa gwamnatin hadin kan kasar, wadda za ta kunshi daukacin sassan kasar ciki hadda mata.
Ya ce ya zama wajibi shuwagabannin kasar ta Somaliya su hada kai da juna, domin cimma nasarar kafa nagartacciyar gwamnatin tarayyar kasar, su kuma tabbatar da nasarar aikin sake nazartar kundin tsarin mulkin kasar.
Game da nasarar da dakarun kungiyar AU da na gwamnatin Somaliyar ke samu kan kungiyar Al-Shabab kuwa, Mr. Ban ya ce ya dace a kara azama, wajen ci gaba da kwazo bisa doka, tare da sake inganta ayyukan da ake gudanarwa. Daga nan sai ya bayyana kudurin MDD na ci gaba da baiwa kasar Somaliya gudummawa, wajen cimma nasarar wanzar da zaman lafiya, tare da tabbatar da kare hakkokin bil'adama a kasar.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 24 ga watan Disambar da ya gabata ne aka rantsar da Sharmarke a matsayin wanda zai maye gurbin Abdiweli Sheikh Ahmed, mutumin da majalisar dokokin kasar ta jefawa kuri'ar rashin amincewa, sakamakon takun sakar da ya ki ci ya ki cinyewa tsakaninsa da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud. (Saminu Hassan)