A gun taron manema labaru na ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kakakin hukumar kididdigar Sheng Laiyun ya bayyana cewa, Sin ta nuna himma da gwazo ta fuskar bunkasa tattalin arziki mai inganci duk da hali mai sarkakiya da tafiyar hawainiyar da bunkasuwar tattalin arziki da ake fuskanta a cikin kasar, a yayin kuma ake mai da muhimmanci sosai kan daga inganci da moriya a fannin bunkasa tattalin arziki, da zura ido sosai kan sauya hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki da yada amfanin kasuwanni, da kuma kara karfin tabbatar da zaman rayuwar jama'a.
An ce, ko da yake Sin na nuna sanyin jiki wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, amma tsare-tsaren masana'antu na samun kyautatuwa sosai. (Amina)