A cewar mataimakin shugaban kwastam na birnin Xi'an, hedkwatar lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin Chen Honggang, saboda aiwatar da shirin Ziri daya da hanya daya, lardin Shaanxi zai bude kofarsa a dukkanin fannoni, ciki hadda hanyoyin kasa, teku da sama. Ban da haka kuma, alfanun da shirin ya kawowa lardin ya yi yawa, alal misali, a shekarar 2014 yawan kayayyakin da lardin ya fitar zuwa yankunan tsakiyar Asiya ya karu da kashi 79.4 cikin dari bisa na shekarar 2013.
A wani bangare na daban, ganin yadda manyan ababen more rayuwa masu inganci suka kasance babban tushe ne ga aikin aiwatar da shirin Ziri daya da hanya daya, lardin Yunnan ya yanke shawarar kara tsawon tagwan hanyarsa zuwa ga kilomita 6000 a shekarar 2020, yayin da tsawon layin dogon dake lardin zai kai kilomita 5000, kana za a kafa hanyoyoin jiragen sama fiye da 410 baki daya.
Bugu da kari kuma, a farkon wannan wata, an fara yin amfani da jirgin kasa na farko da ya tashi daga birnin Wuhan dake tsakiyar kasar Sin zuwa ga kasar Jamus, wanda ke dauke da sundukai 41 na kayayyakin yada bayanai na latironi, kekuna masu karfin wutar lantarki, kayayyakin gilashi da sauransu. Bayan kwanaki 15 kuma ya isa birnin Hamburg inda ake samun tashar ruwa mafi girma a kasar Jamus.
An ce yanzu za a fara yin amfani da wani yankin ajiyar kayayykin kasashen ketare ba tare da karbar haraji ba a kudancin jihar Xinjiang dake yammacin kasar Sin, wanda ya kasance irin wannan yanki na farko a kudancin lardin Xinjing, haka kuma wannan ya kasance daya daga cikin matakan da jihar Xinjiang ke dauka bisa matsayinta na wani muhimmin yanki a kan hanyar siliki da ake kokarin ginawa. (Amina)