Yayin taron na manema labaru, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, ya yi karin haske kan batun, tare da amsa tambayoyi da 'yan jarida suka yi.
Li Baodong ya bayyana cewa, akwai muhimman abubuwa 3 game da taron na shekara-shekara, na dandalin tattaunawar da firaministan Sin Li Keqiang zai halarta. Abu na farko shi ne wannan ne karo na farko da manyan shugabannin Sin za su kai ziyara a kasashen waje a shekarar 2015. Abu na biyu kuwa shi ne shekaru 5 ke nan tun bayan da shugabannin Sin suka halarci dandalin tattaunawar da shude. Na uku kuwa shi ne taron na wannan karo ya fi wadanda aka yi a baya girma.
Ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewa akwai shugabannin kasashe da gwamnatoci kimanin 50, da kuma wakilai fiye da 2500 daga bangaren siyasa, da na 'yan kasuwa, da ilmi da kafofin watsa labaru na kasashe fiye da 140 za su halarci taron.
Bugu da kari Li Baodong ya ce, Li Keqiang zai gudanar da muhimman ayyuka 3 a yayin taron dandalin tattaunawar, da suka hada da gabatar da jawabi a gun cikakken zaman taron tare da amsa tambayoyi, zai kuma tattauna da wakilan majalisar masana'antu, da cinikayya ta kasa da kasa ta dandalin tattaunawar, sa'an nan ya kuma gana da shugaban kwamitin dandalin tattaunawar Klaus Schwab. (Zainab)