in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 7.4 bisa 100 a shekarar 2014
2015-01-20 15:36:57 cri

Bisa rahoton da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fidda a yau Talata 20 ga wata, an ce, ma'aunin tattalin arzikin na GDP na kasar Sin a shekarar 2014 ya kai yuan biliyan 63646.3, adadin da ya karu da kashi 7.4 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2013.

Tattalin arzikin kasar na ci gaba da karuwa cikin yanayin mai kyau da karko, tare da samun kyautattuwa, lamarin da ya tallafawa zaman al'ummar kasar Sin sosai, shugaban hukumar kididdigar kasa ta Sin Ma Jiantang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasa ta Sin ya yi a yau Talata a birnin Beijing. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China