Mr. Zhu Zhixing ya bayyana haka ne a yayin taron sanar da bayanai game da manufofin da gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar. Mr. Zhu ya nuna cewa, a yayin da ake inganta harkokin saye da sayarwa, ana kuma kashe kudi ta hanyoyi iri iri, ko hanyar dake dacewa da halin musamman na mutum daya kawai. Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin za ta kara yin kwaskwarima kan ka'idojin biyan albashi domin kokarin kara yawan kudaden da jama'a ke samu. Sannan, za a kara kyautata tsarin ba da inshora ga zaman al'umma, ta yadda jama'a ba za su damu ba a lokacin da suke kashe kudi. Kazalika, za a kyautata yanayin kashe kudi, ta yadda jama'a za su iya kashe kudi kamar yadda suke so. Daga karshe, za a yi kokarin bullo da sabbin fannoni, game da yadda jama'a suke son kashe kudi. (Sanusi Chen)