in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a kokarta wajen sabawa sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arzikin kasar Sin, in ji Xi Jinping
2014-12-15 14:46:44 cri
Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin a kwanakin baya, ya jaddada cewa, kamata ya yi a kokarta wajen sabawa sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arzikin kasar Sin, bisa ra'ayoyin da aka cimma a yayin taron kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na cikakken zaman taro na 3 da na 4 na kwamitin tsakiya na 18 na JKS, gami da taron ayyukan tattalin arziki na kasar, ta yadda za a sa kaimi ga aikin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje da na raya kasa mai tsarin gurguzu zuwa wani sabon matsayi.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kamata ya yi a dora muhimmanci kan gudanar da ayyukan kiwon lafiya da samar da albarkatun kiwon lafiya a kananan wuraren kasar Sin. Ya kara da cewa, aikin gona dake yin amfani da fasahohin zamani ita hanya ce mafi kyau ga manoma wajen kara samun kudin shiga. Sa'an nan ya kamata a canja hanyar bunkasa tattalin arziki da kyautata tsarinsa domin raya shi yadda ya kamata.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya nanata cewa, ya wajaba a dauki tsauraran matakai wajen gudanar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin domin ci gabanta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China