A yayin wannan taro, an ce, ya kamata a fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa kasashen ketare kamar yadda ake bukatarsu wajen gina kayayyakin kasashen da kuma neman bunkasuwa, sa'an nan gwamnatin ta ciyar da wannan aikin gaba, a yayin da wasu kamfanoni ke gudanar da aikin. Kana, fitar da manyan kayayyaki da kuma fasahohin zamani na kasar Sin zuwa ketare ya dace da moriyar juna, ba ma kawai zai iya habaka damar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ta kasa da kasa ba, haka kuma zai iya kyautata ayyukan masana'antun kasar Sin. (Maryam)