Kundin mai taken 'Ra'ayoyi kan yadda za a kara yin gyare-gyare da kirkiro sabbin fasahohi don raya aikin gona na zamani' ya kunshi kalmomi kimanin 12000, wanda ya shafi fannonin da suka hada da, gaggauta sauya hanyar da ake bi wajen raya aikin gona, da kara daukar matakai don samar da karin kudin shiga ga manoma, da kara gina sabbin kauyuka don kau da gibin dake tsakanin birane da kauyuka, da karfafa gyare-gyare don kara samar da damamakin samun ci gaba a kauyuka, da inganta aikin shari'a a kauyukan kasar.
Ban da haka kuma, cikin kundin an bayyana cewa, tilas a dora cikakken muhimmanci kan ayyukan da suka shafi aikin gona, kauyuka da manoma. Sa'an nan ya kamata a yi amfani da matakan gyare-gyare, gami da bin dokoki, don ciyar da aikin gona gaba, wanda zai dace da tsarin musamman na kasar Sin. (Bello Wang)