Ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da fasahohin ci gaba ta kasar Sin ta kayyade yawan ma'aikatun da ya kamata a rufe cikin shekarar 2014 a farkon shekarar, wanda ya shafi ma'aikatun da suke samar da bakin karfe ton miliyan 28.7 da siminti ton miliyan 50.5, da gilashi na akwatuna miliyan 35 a shekara guda.
A cewar ma'aikatar kula da masana'antun kasar Sin, yanzu irin wadannan ma'aikatu da ke kasar sun fi mai da hankali kan kokarin inganta fasahohinsu bisa la'akari da sabon yanayi na yau da kullum da tattalin arzikin kasar ke ciki. Yanzu jarin da aka zuba a bangaren aikin gyara fasahohi kan dukkan kudin jarin da aka zuba ma masana'antun kasar ya wuce kashi 40%, kuma an cimma nasara sosai a kokarin takaita masana'antu masu amfani da tsoffin fasahohi, yayin da yadda ake kokarin sayen bayanai shi ma yana sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Haka zalika, a cewar ma'aikatar kula da masana'antun kasar Sin, za a kara saurin bunkasa wasu sabbin masana'antu masu alaka da manyan tsare-tsaren kasar a shekarar 2015, kuma za a ci gaba da kokarin takaita masana'antu masu amfani da fasahohi da suka kasance tsohon yayi, a kokarin da ake na canza tsarin masana'antun kasar.(Bello Wang)