in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PWC: Mai yiwu kasar Sin za ta zama kasuwar sayar da kayayyaki mafi girma a shekarar 2018
2015-02-13 16:05:05 cri

Daya daga cikin manyan kamfanoni hudu mai aikin akanta a duniya wato Pricewaterhouse Coopers ya ba da wani rahoto na hasashe a jiya Alhamis 12 ga wata cewa, Sin za ta zama kasuwar sayar da kayayyakin da bana sari ba mafi girma a duniya nan da shekara ta 2018.

Rahoton ya ce, ko da yake saurin bunkasuwar wannan fanni a kasar Sin ya nuna sanyin jiki bisa ga matakin kolin da ya kai a shekarar 2009 da kashi 15 cikin dari, amma idan an kwatanta da sauran kamfanonin kasa da kasa, Sin ta kasance wata kasuwa dake jawo hankalin kasashe daban-daban. A cikin shekaru biyu masu zuwa, saurin bunkasuwa a wannan fanni zai kai kashi 8.7 cikin dari.

Mai hada kai da babban jami'in wannan kamfani dake kula da harkokin kayayyaki da bana sari ba da kayayyakin more rayuwa a nan kasar Sin Mr Wang Xiao ya nuna cewa, tun daga wannan shekarar da muke ciki, bunkasuwar tattalin arzikin Amurka da farfadowar tattalin arzikin yankunan dake yin amfani da kudin Euro, ko da yake yana fuskantar matsi, za su sa kaimi ga bukatunsu na sayan kayayyki daga Asiya. Ya kuma yi hasashen cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, yawan kayayyakin da yankin Asiya za ta sayar zai sami bunkasuwa mafi sauri a duniya. Hakan ya sa Sin za ta fuskanci tafiyar hawainiya ta fuskar saurin bunkasuwar tattalin arzikin a sakamakon bunkasuwar kasuwannin ta nan gaba.

Domin ganin haka, kamfanoni masu sayar kayayyakin da bana sari ba za su kyautata tsarinsu, kamar rufe wasu kantuna, ko hadewa da wassu da kuma janye jiki daga kasuwa. Kazalika, Mr Wang ya ce, wadannan kamfanoni za su kyautata tsarin su don ganin hadewar sha'anin yin ciniki na intanet da na salula. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China