Jakadan kasar Sin dake Ghana Madam Sun Baohong, babban sakataren kungiyar sada zumunci tsakanin Sin da Ghana da kuma ma'aikatan kamfanoni masu jarin kasar Sin a Ghana da dalibai da malamai sun kalli gasar da aka yi a Asabar 11 ga wata.
Gasar a wannan karo ya kasu kashi uku, wato jarrabawar takardu, yin jawabi da nuna fasahohin al'adu. Bayan takara mai tsananin da aka yi, wata 'yar takara mai suna Jiali da Sinanci daga jami'ar Ghana ta samu matsayin farko a gasar, wadda kuma ta samu damar shiga gasa ta karshe da za a gudana a kasar Sin. (Amina)