An ce, kasar Madagascar na fama da bala'in mahaukaciyar guguwa da ruwan sama mai karfin gaske, wadanda suka lalata wasu madatsan ruwa, hanyoyi, gadoji, gidaje da dai sauran manyan ababen more rayuwa. Ban da haka kuma, hedkwatar kasar Antananarivo na fama da bala'in sosai, ruwan sama ya shafe wasu wurare da babu tsayi. Hakan ya sa, mutane fiye da dubu 60 suke cikin mawuyacin hali, 24 ya zuwa yanzu sun rasa rayukansu, kuma mutane fiye da 30,000 sun rasa gidajensu.
Saboda ganin irin bala'i mai tsanani da kasar Madagascar ke fuskanta, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar samarwa kasar tallafin kudi dala dubu 300 don taimakama gwamnatin Madagascar wajen gudanar da ayyukan ceto. (Amina)