Ya zuwa karfe 6 na daren ranar 26 ga wata, hukumar zaben kasar ta gabatar da sakamakon tasoshin jefa kuri'u guda 366, duk da cewa jimilar tasoshin jefa kuri'u a kasar ta kai 20,001. Babban sakataren hukumar Jean Victor Rasolonjatovo ya ce, ana bukatar kowace tashar jefa kuri'u da ta aika sakamakon kidaya kuri'unta zuwa hukumar zaben kasar, amma matsalar ita ce wasu yankuna ba su da hanyoyin sufuri masu kyau , shi ya sanya ana bukatar kwanaki 7 zuwa 10 don tattara da kidayar dukkan kuri'un zaben.
Bisa sakamakon kidaya kuri'un da aka samu a halin yanzu, an ce, dan takara Jean Louis Robinson da tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana ke nuna goyon baya da tsohon ministan kudi na kasar Hery Rajaonarimampianina suke a sahun gaba. Amma manazarta sun nuna cewa, ganin akwai 'yan takara da dama, abin zai yi wuya a samu wani dan takara da zai samu kuri'u fiye da rabin yawan kuri'un zaben a zagayen farko, don haka akwai yiwuwar zagaye na biyu. (Zainab)