Bayan nada sabbin ministoci, firaminista Roger ya bayyana cewa, babban makasudinsu shi ne kawo alheri ga jama'ar Madagascar da yawansu ya kai miliyan 22. Babban aikin ministocin shi ne tabbatar da bunkasuwar kasar, ta yadda za a cika alkawarin da shugaban kasar ya yi a yayin babban zaben.
A watan Disamba na shekarar 2008, tsohon magajin garin birnin Tananarive, Andry Nirina Rajoelina da magoya bayansa sun yi ta zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin kasar, lamarin da ya kai ga wasu sojoji suka karbe mulki. Daga bisani, tTsohon shugaban kasar Madagascar Marc Ravalomanana ya sanar da yin murabus a watan Maris na shekarar 2009, tare da barin kasar. A ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2009, bisa goyon bayan sojasojojin kasar, Andry Nirina Rajoelina ya zama shugaban gwamnatin rikon kwarya. A watan Disamban bara, kasar Madagascar ta gudanar da zaben shugaban kasar cikin nasara, kuma wannan ya ba da taimako sosai wajen daidaita rikicin siyasa a kasar.(Fatima)