in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba da yadda aka kammala zaben kasar Madagaska lami lafiya
2013-12-21 16:21:58 cri
Babban magatakarda na MDD Ban Ki-moon ya jinjinawa mahukunta da hukumar zabe da ma daukacin al'ummar kasar Madagaska, bisa kammalar babban zaben kasar na ranar Jumma'a lami lafiya. Mr. Ban ya kara da kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a kasar, da su tabbatar da dorewar kyakkawan yanayin da kasar ke ciki.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar, Ban ya bukaci gwamnatin rikon kwarya, da ma masu fada-a-ji na jam'iyyun siyasar kasar, da su kasance masu goyon bayan doka da oda, yayin da ake kidaya, ya zuwa lokacin da za a fayyace sakamakon zaben. Ya ce, MDD za ta ci gaba da kasancewa mai tallafawa shirin mika mulkin kasar ga zababbiyar gwamnatin. Har ila yau Mr. Ban ya jaddada bukatar martaba muradan daukacin al'ummar kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China