Shugaba Hery Rajaonarimampianina ya ce, mambobin majalisar 93 ne suka amince da nadin Dakta Kolo Roger a matsayin firayin ministan kasar daga cikin yayan majalisar 151.
Shugaba Rajaonarimampianina ya yi fatan mambobin majalisar dokokin kasar ta Madagascar, wadanda ke goyon bayan tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Andry Rajaoelina, za su bayar da hadin kai ga sabon firayin ministan kasar.
Shugaban ya kara da cewar an gudanar da nadin Roger kamar yadda dokar tsarin mulkin kasar ta tanada, tana mai cewar "Shugaban yanki shi ne zai nada sabon firayin ministan tare da la'akari da mubaya'a na jerin jam'iyya ta siyasa, ko kuma wani gungun na jam'iyyun siyasa wadanda suke da rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Shugaban ya ce za'a kafa sabuwar gwamnati nan da mako guda, sai dai shi sabon firayin ministan da aka nada, watau Dakta Kolo Roger bai halarci bukin nadin nashi ba. (Suwaiba)