A ran 25 ga wata, sabon shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina ya yi rantsuwar kama aiki. Bayan ya yi rantsuwa ba da jimawa ba, an tada wata fashewar gurnet a wurin da ya yi rantsuwa, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 1, tare da jikkata saura fiye da 30, dukkansu mazaunan wurin ne.
A ran 25 ga wata da safe, Rajaonarimampianina ya yi rantsuwar kama aiki a cikin wani ginin wasanni da ke dab da harabar majalisar dokokin kasar, wasu shugabannin siyasa na kasashen Afirka sun halarci bikin. Rajaonarimampianina ya yi wani jawabi bayan kammalar bikin cewa, ya kamata rukunoni daban daban na siyasa su hada kansu, don yin kokarin samar da wata kyakkyawar makoma ga kasar Madagascar. A ran 24 ga wata, shugaban wucin gadi na kasar Andry Rajoelina ya mayar da ikon shugabancin kasar a hannun Rajaonarimampianina.
A daidai wasu sa'o'in da aka gama bikin rantsuwa, an tada wata fashewa a gaban harabar majalisar dokokin kasar. 'Yan sandan sun ce, wani namiji ya jefa gurnet zuwa tarin jama'a, wanda ya sanya mutane fiye da 30 suka ji rauni, wani yaro ya rasu bayan da aka kai shi asibiti, kuma mutane 10 da ke cikinsu suka ji rauni mai tsanani.
Yanzu ba a tabbatar da dalilin da ya sanya wannan fashewa ba, amma ba a iya kawar da dalilin siyasa ba.
A ran nan ne, Rajaonarimampianina ya je asibiti ya gana da wadanda suka ji rauni, inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ba za ta yi hakuri da karfin tuwo ba, za ta bincike kan lamarin, da gurfanar da masu laifin a gaban kuriya. (Danladi)