in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan takarar zaben shugaban kasar Madagascar ya bukaci a sake kidaya kuri'un da aka kada
2013-12-24 11:50:53 cri
Ran 23 ga wata, dan takarar zaben shugaban kasar Madagascar Jean-Louis Robinson ya ki amince da sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta gabatar, bisa dalilin cewa an aikata magudi yayin babban zaben shugaban kasar, kuma zai daukaka kara a gaban koton musamman mai kula da harkokin zabe.

Bisa sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta gabatar a ran 23 ga wata, an ce, Jean-Louis Robinson ya samu kashi 47.85 cikin 100 a yayin da abokin takararsa, Hery Rajaonarimampianina ya samu kashi 52.15 cikin 100, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka shirya a ranar 20 ga wata.

Amma a yayin taron manema labarai da aka yi a birnin Antananarivo, Mr. Robinson ya tabbatar da cewa, yawan kuri'un da ya samu ya haura kashi 50 cikin dari, don haka, ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar da ta sake kidaya kuri'un. Ban da wannan kuma, zai daukaka kara a gaban koton musamman mai kula da harkokin zabe, saboda magudin da ya ce an tabka a wasu tashoshin kada kuri'u.

'Yan Madagascar na zaben shugaban kasar zai warware rikicin siyasar kasar, kana dukkan 'yan takarar da suka shiga zaben da aka yi a watan Oktoba na bana ba su yi nasanar samun rabin kuri'un da aka kada ba, don haka, 'yan takara guda biyu wadanda suke kan gaba watau Jean-Louis Robinson da kuma Hery Rajaonarimampianina ne suka shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China