in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Madagascar
2013-12-20 20:10:54 cri
Rahotanni daga kasar Madagascar na cewa, a ranar Jumma'a ne aka fara zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, inda ake fatan sabon shugaban da za a zaba, zai fitar da kasar da ta shafe shekaru biyar tana fama da rikicin siyasa.

Shugabar hukumar zaben kasar mai zaman kanta(CENI-T) Atallah Beatrice, ta shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin da take duba yadda zaben ke gudana a rumfar zabe ta Alarobia cewa, an fara zaben a baki dayan rumfunan zaben kasar 20,001 yadda ya kamata.

Ta bayyana cewa, tun daga karfe 5 na safe agogon wurin wasu rumfunan zabe suka bude wato sa'a guda kafin lokacin bude rumfunan a hukumance.

A wannan rana ne kuma ake gudanar da zabukan 'yan majalisun dokokin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China