Shugabar hukumar zaben kasar mai zaman kanta Atallah Beatrice, ta bayyana a ranar Jumma'a yayin wani taron da ya samu halartar jami'an gwamnati, 'yan takarar mukamin zaben shugaban kasar da 'yan kallo na kasa da kasa cewa, Hery Rajaonarimampianina, ya samu kashi 53.50 na kuri'un da aka kada, yayin da abokin takararsa Jean Loius Robinson ya samu kashi 46.50 cikin 100.
Bisa dokar kasar, za a gabatarwa kotun musamman mai kula da harkokin zabe(CES) sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana, inda kotun za ta yanke hukunci kan dukkan koke-koken zaben da aka gabatar mata cikin kwanaki 15 kana ta bayyana sakamako na karshe.
Sai dai Jean Robinson ya kokawa kotun ta CES cewa, an tabka magudi yayin zaben, ko da ya ke 'yan kallo na kasa da kasa da suka ido a zaben, sun ce zaben ya tafi dai-dai.(Ibrahim)