Babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa ta bakin kakakinsa a daren Asabar 18 ga wata, inda ya yi maraba da shawarar da kotun musamman mai kula da harkar zabe ta kasar Madagascar ta yanke kan sakamakon zaben shugaban kasar, tare kuma da yin kira ga shugabannin kasar da su tabbatar da samun sulhuntawa tsakaninsu.
Ban Ki-Moon ya yi kira ga dukkan 'yan takarar shugaban kasar da su mutunta matakin kotun ta yanke, da kuma bayyana ra'ayoyinsu bisa hanyar da ta dace cikin lumana. Ban da haka, ya yi kira ga sabuwar gwamnatin kasar da ta yi mu'ammala da jam'iyyun adawa, da biyan bukatun daukacin jama'ar kasar yayin da take gudanar harkokin kasar.
Kotun ta yanke shawara a ran 17 ga wata cewa, Hery Rajaonarimampianina ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu na watan Disamba na bara. (Amina)