in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da takwaransa na Madagascar
2014-08-28 20:23:12 cri
A yau ne firaministan kasar Sin Li keqiang ya gana da takwaransa na kasar Madagascar Kolo Roger wanda ya zo kasar Sin don halartar bikin rufe gasar Olympics ta matasa a birnin Nanjing.

Yayin ganawarsu, Li keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin makamashi, noma, kiwon dabbobi da kiwon kifi, kawar da talauci da dai sauransu. Haka kuma kasar Sin tana goyon bayan kasar Madagascar kan kafu yankin cinikayya da na masana'antu, da kuma raya harkokin sadarwa na zamani da sufuri, don taimakawa kasar wajen neman hanyoyin bunkasuwa da kanta.

A nasa tsokaci, Kolo Roger ya ce, jama'ar kasarsa na daukar al'ummomin Sin tamkar 'yan uwansu, haka kuma, kasar Madagascar tana son karfafa mu'amalar dake tsakaninta da kasar Sin bisa fannoni daban daban don cimma moriyar juna. Bugu da kari, al'ummomi da kamfanonin kasar Sin dake kasar Madagascar dukkansu sun ba da gudumawa sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wannan ya taimaka ga jin dadin zaman rayuwa da ayyukan al'ummar Madagascar (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China