Robinson ya nuna wa manema labarai wasu ambulan kunshe da wasu takardun sakamakon zaben da aka like daga tashoshin zabe da za a aika wa hukumar zaben kasar, matakin da dan takarar ya ce abu ne da ba za a lamunta ba.
Ya ce magoya bayansa za su fito kan tituna su yi zanga–zanga, amma za su tsaya ne wurin da za su yi taro, domin su nemi 'yancinsu.
Shugaban kotun musamman mai kula da harkokin zaben kasar ce Rakotozafy Francois ya bayyana sakamakon zaben a safiyar ranar Jumma'a, inda ya nuna cewa, Hery Rajaonarimampianina ne aka zaba a matsayin shugaban kasar ta Madagascar ta kashi 53.49 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Jean Robinson ya samu kashi 46.51 cikin 100. (Ibrahim Yaya)