in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kame tsohon shugaban kasar Madagaska jim kada da dawowar sa gida daga gudun hijira.
2014-10-13 20:57:11 cri
Bayan dawowarsa gida da safiyar nan tare da shirya taron manema labarai a garinsa dake Antananarivo, babban birnin kasar Madagaska, jami'an tsaro sun yi awon gaba da tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana kamar yadda magoya bayansa suka shaida ma kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua.

Bayan taron manema labaran, tawagar sojoji suka far ma harabar gidan tare da jefa barkonon tsohuwa ta ko ina domin kore magoya bayan shi, sannan suka kame shi da karfin tuwo aka saka cikin mota, kamar yadda tsohon dan majalissar dokokin kasar kuma daya daga cikin magoya bayan shi Tomiara ya yi bayani.

A harabar gidan za'a iya ganin windunan da aka fasa da alamun hujin harsashi da aka harba jikin gidan.

Sai dai ya zuwa karfe sha dayan safe agogon kasar, Hery Rajaonarimampianina, shugaban kasar Madagaskan na yanzu ya sake yin bayani a shafin sa na Facebook cewa ana kokarin sulhunta 'yan kasar ne da zummar kawo cigaba a Madagaskar.

A shekara ta 2009, Marc Ravalomanana ya tafi gudun hijira a kasar Afrika ta kudu bayan da aka tilasta shi mika mulki ga sojoji sakamakon gaggarumin bore da Andry Rajoelina Magajin garin Antananarivo a wannan lokacin ya jagoranta wanda daga bisani ya zama shugaban kasar na rikon kwarya kafin babban zabe a bara.

Bayan zaben ne aka rantsar da Hery Rajaonarimampianina a watan Janairun wannan shekarar tare da kafa gwamnati da majalissar dokoki. (Fatimah Jibri)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China