Mr. Abadi ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, lokacin da ya ziyarci Erbil, babban birnin yankin Kurdawa, inda ya yi shawarwari tare da shugaban yankin Massoud Barzani game da hakan.
Bayan kuma kammala shawarwarin nasu, Mr. Abadi ya bayyana wa wani taron manema labaru cewa, gwamnatin kasar Iraqi, da gwamnatin yankin Kurdawa sun kafa wani kwamitin hadin gwiwa, domin gudanar da ayyukan soji a kokarinsu na kwato lardin Nineveh.
Bugu da kari, Abadi ya ce, gwamnatin Iraqi da gwamnatin yankin Kurdawa sun riga sun cimma ra'ayi daya game da jadawalin daukar matakan soja, ko da yake bai yi karin bayani game da jadawalin ba. (Maryam)