in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Iraqi sun kai hare-hare ga IS
2014-11-19 15:47:04 cri
Wata majiya ta sojin kasar Iraqi ta bayyana a ran 18 ga wata cewa, rundunar tsaron kasar ta Iraqi ta mai da martani kan reshen kungiyar IS wanda ya mamaye Saadiya, wani muhimmin birnin dake gabashin Iraqi, haka zalika sojojin gwamnatin kasar sun karbe wani garin dake kusa da ma'aikatar tace mai ta birnin Baiji.

Ministan tsaron kasar Iraqi Khaled al-Obaidi ya sanar a ran 18 ga wata cewa, Iraqi na kin amincewa da duk wata rundunar kasashen waje da ta shiga kasarta bisa dalilin yaki da ta'addanci, tare da jaddada karfin kasar da take da shi wajen yaki da ta'addanci. Ya ce, rundunar kasa za ta dauki nauyin kai farmaki domin murkushe IS.

A nata bangare, mataimakiyar direkta mai kula da harkokin jin kai na MDD Valerie Amos ta nuna a ran 18 ga wata a birnin New York hedkwatar MDD cewa, halin jin kai a Iraqi ya kara tsananta, a don haka abin da ya kamata a yi yanzu shi ne kiyaye zaman lafiyar fararen hula. Ta ce, dakarun IS sun fi kai kai hare-hare kan fararen hula a Iraqi, amma ba kungiyar ita kadai ke keta hakkin bil Adam ba, akwai kuma sauran kungiyoyin masu dauke da makamai da suke kai hare hare kan fareren hula a kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China